An dade ana muhawara a tsakanin masu sana’a da masu digiri, musamman wadanda suka yi gam-da-katar suka samu ayyuka masu tasiri, kan abin da ya fi kawu samu.
Ko wanne bangare yana da kwararan hujjoji; amma masu raba gardama sun ce akwai zabi na uku.
Shin wanne zabi ne wannan?
Abin da shirin Daga Laraba zai yi nazari a kai ke nan.