Madubin Usman Kabara: Tallan Zango Na 1
Daga yanzu Madubin Usman Kabara podcast zai dinga zuwa muku ne a tsarin shiri mai fitowa zango-zango, inda zamu saki zangon na 1 a mako mai zuwa ranar Juma’a 9 ga watan Janairun shekarar nan ta 2026. Kadan daga cikin bakin wannan zangon sun hada da:1. Prof. Abdalla Uba Adamu2. Umar M. Shareef3. Hon. Zainab Buba 4. Hon. Saudatu Sani5. Maryam Booth6. Zaaki AzzayKu yi following dina ta nan a kyauta don jin yadda mutane ke shan gwagwarmaya a rayuwa don mu koyi darasi ta hanyar ganin zurfin ruwa da na gaba.
Solomon Dalung | MUK Na 39
Na sami zama tare da Lauya Dan Gwagwarmaya Barrister Solomon Dalung, tsohon Ministan Matasa Da Wasanni a lokacin mulkin Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari. Inda na tattauna da shi don kallon rayuwarsa a cikin shirin Madubin Usman Kabara Podcast domin daukar darasi ga ‘yan baya.
Usman SojaBoy | MUK Na 38
Na ziyarci Usman Umar (SojaBoy), domin yin hira da shi ido da ido a kokarina na jin dalilan salon wakokinsa da mafiya yawan mutane musamman 'yan Arewacin Najeriya, ba su yarda da salon nasa ba, suna ma kallon abin a matsayin rashin tarbiyya da rushe al'ada da addini.
Nazir Hausawa (Ziriums) | MUK Na 37
Nazir Ahmed Hausawa (Ziriums), yana daya daga cikin ‘yan masana’antar finafinan Kannywood, Makadin Fiyano, Mawakin gambarar Hausa HipHop, Tsohon malamin koyar da kida, Tsohon ma’aikacin BBC World Service Trust da VOA Hausa, Masanin harkokin gidajen alfama na Amurka. A cikin hirarsa da Madubin Usman Kabara a Amurka, ya bayyana min darussan da ya koya a zamansa na shekaru a Amurka.
Nafisat Abdullahi | MUK Na 36
Na sami yin hira da shahararriyar Jarumar Fina-finan Hausa Nafisat Abdullahi a birnin Washington DC da ke Amurka, don sanin asalinta da kuma yadda take tafiyar da rayuwarta.