Dalilan Da Suka Sa Matan Wannan Zamanin Ba Sa Son Talaka
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa. Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi. Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta mai abin hannu.Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan matan wannan zamanin na kin auren talaka.
Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya
Rage farashin man fetur a Najeriya na daya daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin al’umma, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ta yi wa ’yan kasa katutu a ‘yan watannin nan. Man fetur ba wai kawai makamashi ba ne da ake amfani da shi wajen tafiyar da ababen hawa; ginshiki ne da kusan dukkan harkokin tattalin arziki ke jingina da shi – daga sufuri, da samar da kayayyaki, har zuwa rabon su zuwa kasuwanni.Saboda haka, duk wani sauyi a farashin mai kan yi tasiri kai tsaye ko a kaikaice ga farashin kayan masarufi da ’yan Najeriya ke amfani da su a kullum, kamar abinci, da kayan gini, da magunguna da sauransu. Sai dai tambayar da ke yawan fitowa ita ce: shin rage farashin mai zai kai ga rage farashin wadannan kayayyaki? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan kare dangi ga Najeriya.Ko wannan ziyarar da tawagar Amurka ta kawo zai kawo karshen matsalar tsaron da Najeriya ke ciki?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba a kai.
Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa majalisar.Wannan naɗin ya zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman hare-haren ’yan bindiga, da ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci a yankuna daban-daban.Ko wadanne irin kalubale ne ke gaban sabon ministan tsaron yayin da yake shirin kama aiki a ma’aikatar tsaro bayan majalisa ta tabbatar da shi?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
A cikin 'yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da 'yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi.Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu?Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a akai.