Manufar wannan shiri shi ne koya wa masu sauraronmu girke-girke na Sinawa masu sauki, wadanda kuma ake iya samun kayan hadasu a kasashen Afrika, musamman inda muke da rinjayen masu sauraronmu a harshen Hausa. Sanin kowa ne Sinawa suna da wasu dabaru masu ban sha’awa na sarrafa abinci mai dadin gaske, da suka hada da ganyaye, da kayan lambu, da kayan marmari, da ma sauran nau’o’in hatsi. Bugu da kari irin yadda aka san su da noman shinkafa kanshi, a hannu guda akwai dabarun sarrafa wannan abinci ta hanyoyi masu daman gaske.
view more